1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin ƙasar Holland ta rushe.

YAHAYA AHMEDJune 30, 2006

Fiiramiyan ƙasar Holland, Jan Peter Balkenende ya ba da sanarwar miƙa takardar murabus ɗin gwamnatinsa ga Sarauniyar ƙasar. Hakan kuwa ya zo ne bayan wani rikicin da ya janyo janyewar jam’iyyar D66 daga gwamnatin haɗin gambizar. Asalin wannan rikicin kuwa, shi ne saɓanin da aka samu tsakanin jam’iyyun biyu, game da batun janye wa wata tsohuwar ’yar majalisa mai asali daga Somaliya, kuma mai sukar manufofin addinin islama, Ayaan Hirsi Ali, takardunta na zama ’yar ƙasar Holland ɗin, saboda zargin da ake yi mata na labta ƙarya a lokacin da ta zo neman mafaka a ƙasar.

https://p.dw.com/p/BtzV
Firamiya Balkenende da ministan harkokin cikin gidansa, Rita Verdonk
Firamiya Balkenende da ministan harkokin cikin gidansa, Rita VerdonkHoto: AP

Tun ran larabar da ta wuce ne dai aka yi ta yaɗa raɗe-raɗin cewa, wani sabon rikici na kunno kai a gwamnatin haɗin gwiwa ta ƙasar Holland. Amma babu wanda ya yi hasashen cewa wannan rikicin zai janyo rushewar gwamnatin gaba ɗaya. Su ’yan ƙasar Holland din ma dai na bayyana ra’ayoyi daban-daban ne a kan wannan batun. Wasu mutane da aka yi fira da su, sun bayyana ra’ayinsu ne kamar haka:-

„Miƙa takardar murabus ɗin da Balkenende ya yi, abin kirki ne. Ya dai cancanci wannan sakamakon.“

„A nawa ganin dai, abin ban takaici ne, saboda laifin gwamnatin shekaru 4 da suka wuce ne ya shafi wannan gwamnatin.“

Ba mu dai da wata gwamnatin kirki, sabili da haka murabus ɗin ba wani al’ajabi ba ne. Amma abin da nake mamaki a kansa shi ne, a yi ta yayata abin da bai taka kara ya karya ba.“

„Murabus din ya dace. Sun kyauta da suka yi haka.“

A yau ne dai ministoci biyu na jam’iyyar D66 da ke cikin gwamnatin ƙawance ta ƙasar suka ba da sanarwar fitarsu daga gwamnatin. Daga bisani ne kuma, Firamiyan ƙasar, Jan Peter Balkenende, ya bayyana wa majalisa cewa, wannan matakin ya shafe shi da majalisar ministocinsa, abin da ke nufin gwamnatin ta wargaje ke nan. Firamiya Balkenende, ya ƙara bayyana cewa:-

„A matsayin Firamiya, zan miƙa wa sarauniya takardar murabus ɗina. Mai martaba sarauniya, za ta yi shawarwari da manyan masu ba ta shawara. Daga bisani ne kuma za a ba da sanarwar matakan da za a ɗauka nan gaba. Mai yiwuwa a tsai da sabon lokacin zaɓe.“

Masharhanta dai na ganin cewa, Firamiyan ya daɗe yana goyon bayan matakan da ministan harkokin cikin gida da na cuɗanyar jama’a, Rita Verdonk, ke ɗauka. Da ma can, ba ta da farin jini. Sai kuma ga taɓargazar nan ta tsohuwar ’yar majalisa Ayaan Hirsi Ali ta shafe ta: ministan ce dai ta ba da umarnin janye wa ’yar majalisar, mai asali daga Somaliya, Pasfot ɗinta na ƙasar ta Holland, saboda zargin da ake yi mata na yin ƙarya a lokacin da take cike takardun neman zama ’yar ƙasar a shekarar 1997. Amma bayan adawar da ɓangarorin siyasa da dama suka nuna ga wannan matakin, sai ministan ta yi wa shawarar da ta yanken juyin waina.

Game da hakan ne dai wata muhawara mai tsanani ta ɓarke a majalisar dokokin ƙasar da ke birnin Den Haag, inda a ran larabar da ta wuce, shugabar reshen jam’iyyar D66 a majalisar, Lousewies van der Laan, ta yi kira ga ministan da ta yi murabus:-

„Wannan dai batu ne mai muhimmanci ƙwarai da gaske. Ministan ta ƙi amincewa da yin kuskure, duk da sanin kowa a zahiri cewa, halin da ta nuna bai cancanta ba. Ta yi amfani ne da wata, don kambama kanta a fagen siyasa. A namu ganin dai, ta wuce gona da iri. Sabili da haka ne za mu janye amincewarmmu da ita.“

A bukatun da jam’iyyun adawan suka gabatar wa majalisa na neman ka da ƙuri’ar ƙin amincewa da gwamnatin, ba su sami nasara ba. To amma ita shugaban reshen jam’iyyar D66 ɗin a majalisa, van der Laan, ba ta saduda ba. Sai da ta yi ta angaza wa ministocin jam’iyyar guda biyu, har suka bayyana janyewarsu daga gwamnatin jiya alhamis, abin da kuma ya janyo wargajewarta.

Wannan dai shi ne karo na biyu tun shekara ta 2002, da Balkenende, zai rusa majalisar ministocinsa. Bisa tsari dai, da sai cikin watan Mayu mai zuwa ne za a gudanad da zaɓe a ƙasar ta Holland. Amma saboda halin da aka shiga ciki yanzu, mai yiwuwa a kira sabon zaɓe a cikin watan Oktoba ko kuma Nuwamba na wannan shekarar. Jam’iyyun adawan dai na kyautata zaton samun nasara a wannan karon, idan aka yi la’akari da sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kwanakin baya.