Gwamnati ta tsawaita dokar ta baci a Nijar | Labarai | DW | 16.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnati ta tsawaita dokar ta baci a Nijar

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sake tsawaita dokar ta baci a yankin jihar Diffa da ke gabashin kasar da kuma yankin yammacin kasar inda nan ma ake fama da matsalar mayakan jihadi daga Mali.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou (F. Batiche/AFP/Getty Images)

Shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamdou

Sanarwar gwamnatin ta Nijar ta ce, an kara tsawaita dokar ta bacin ne da watanni uku wadda kuma za ta soma daga ranar Litinin 18 ga wannan wata na Satumba a yankin jihar Diffa mai makwabtaka da Jihar Borno a Tarayyar Najeriya ganin yadda har yanzu harkokin tsaro suke da rauni. Sanarwar ta kara da cewa, a yankin yammacin kasar ma an kara tsawaita dokar ta bacin ta tsawon watanni uku, ganin yadda ake ci gaba da samun barazanar 'yan ta'adda da ke fitowa daga kasar Mali.