1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati na shirin yin murabus a Venezuela

Gazali Abdou TasawaDecember 9, 2015

Shugaba Maduro ya yi kira ga majalisar ministocinsa da ta yi murabus bayan shan kaye a zaben 'yan majalisa,don sake kafa sabuwa da za ta farfado da martabar kasar

https://p.dw.com/p/1HJcl
Venezuela Wahlen Nicolas Maduro
Hoto: Reuters/Miraflores Palace

Shugaban kasar venuzuela Nicolas Maduro ya yi kira ga majalissar ministocin gwamnatinsa da ta yi murabus domin sake yin gyara da aiwatar da sauye-sauye da za su sake farfado da martabar gwamnatin kasar baki daya.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da jam'iyyar sa ta PSUV ta sha kayi a zaben 'yan majalisar dokoki wanda jam'iyyar adawa ta MUD ta lashe a karo na farko a cikin shekaru 16 na baya bayan nan.

Yanzu haka dai jam'iyar adawar ta samu kujeru 112 wato kashi biyu daga cikin uku wanda zai bata hurumin iya sake yi wa kundin tsarin milkin garan bawul ko kuma ma takaice wa'adin milkin shugaban mai ci da dai sauran sauye-sauye na tsarin tafiyar kasar