1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnati da yan tawayen Sri Lanka sun cimma yarjejeniya taron zaman lafiya.

Gwamnatin kasar Sri lanka da kungiyar yan tawayen Tamil Tigers sun cimma yarjejeniya ta gudanar da taron wanzar da zaman lafiya a kasar Switzarland a watan gobe. Wani jakadan kasar Norway shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan ganawa da wakilai daga bangarorin biyu. Tun da farko yan kungiyar tawayen na Tamil Tigers sun bukaci gudanar da taron ne a birnin Oslo wanda gwamnatin taki amincewa da shi. An baiyana fargabar cewa takadamar ka iya maida bangarorin biyu cikin wani yakin basasar. Tun a shekara ta 2002 ake ta kokari domin dorewar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu sai da kuma a hannu guda ringingimun da suka taso na baya bayan nan na yin baraza ga shirin samar da zaman lafiyar.