1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwaman Kano ya soki lamirin tafiyar hawainiya ta aikin rejistar masu kuriá

Gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya baiyana tafiyar hawaniyar da aikin sabunta rajistar masu kada kauria ke yi da cewa abu ne dake da tsoratarwa. Malam Shekarau wanda ya sanar da hakan a zantawar da yayi da gidan Radion Deutsche Welle ya yi fatan gwamnatin tarayya zata gaggauta kai dauki ga hukumar zabe ta hanyar samar da naurorin aikin cikin nasara. Yace yin hakan shi ne zai baiwa kowane dan kasa wanda ya kai shekarun yin zabe damar karbar katin rajistar.