1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwajin jini kan harin makami mai guba a Siriya

Zulaiha Abubakar
April 12, 2018

Kasar Amirka ta sanar da samun sinadarin Chlorine cikin gwajin jini da fitsarin wasu daga cikin al'ummar kasar Siriya sakamakon harin makami mai guba da ake zargin gwamnatin Siriyan da kai wa.

https://p.dw.com/p/2vxJE
Syrien Mutmaßlicher Giftgasangriff in Duma
Hoto: Reuters/White Helmets

Harin dai ya harzuka manyan kasashen duniya ciki kuwa har da Faransa, wadanda su ka dauki aniyar mayar da martani. Sai dai tuni Rasha da ke zaman babbar kawa ga gwamnatin shugaba Assad na Siriya  ta musanta hannun gwamnati a harin, kana ta sha alwashin kare duk wani hari da Amirka da kawayenta ka iya kaddamar wa a Siriyan.