1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwagwarmayar kama madafun iko a Zimbabe

September 17, 2010

Rahotanni sun ce ana fama da gwagwarmayar neman gadon kujerar shugabancin Zimbabwe daga Robert Mugabe

https://p.dw.com/p/PFDq
Shugaba Mugabe lokacin bikin shekaru 29 da 'yancin kan ZimbabweHoto: AP

Ko da yake a wannan makon ma kamar yadda aka saba jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al'amuran Afirka, amma zamu fara ne da ya da zango a nan Jamus, inda a wannan makon 'yan sanda suka cafke wata 'yar Nijeriya da ake tuhuma da aiwatar da tsafi domin tilasta wa 'yan mata karuwanci. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar General Anzeiger 'yar birnin Bonn cewa tayi:

"Bisa ga dukkan alamu dai wannan matar ba ita ce kaɗai ke tafiyar da wannan harka ba, tana da abokan hulɗarta dake mara mata baya. Bayanai sun nuna cewar akan kai 'yan mata wurin masu tsafi inda zasu yi alƙawarin mayar da dukkan bashin da aka yi akansu domin shigo da su Turai, abin da galibi ya kan kama kwatankwacin Euro dubu hamsin ko fiye da haka. Kuma duk wadda tayi kurarin kai ƙara gun mahukunta bala'i zai rutsa da ita. Ta haka 'yan matan ke mata biyayya sau da ƙafa. A dai halin da ake ciki yanzun 'yan sanda na bin diddigin lamarin domin gano dukkan masu hannu a wannan ɗanyyen aiki."

A ƙasar Zimbabwe kowane daga cikin muƙarraban shugaba Robert Mugabe ɗan shekaru 86 da haifuwa dake fama da rashin ƙoshin lafiya, ya fara jan daga a gwagwarmayar kama madafun ikon bayan mutuwar shugaban. A lokacin da take ba da wannan rahoton jaridar Neues Deutschland cewa tayi:

"Daga cikin masu fafutukar gadar kujerar ta shugaba Mugabe har da ministan tsaro Emmerson Mnangagwa da tsofon hafsan-hafsoshin soja Solomon Mujur, wanda matarsa ce mataimakiyar shugaban ƙasa yanzu haka. Dukkansu biyu suna wa shugaba Mugabe biyayya sosai-da-sosai. A sakamakon matsin lamba daga Afirka ta Kudu za a gudanar da sabon zaɓe a Zimbabwe shekara mai zuwa. Amma kuma tuni shugaba Mugabe, wanda rashin lafiyarsa ke daɗa tsamari, ya bayyana niyyarsa ta sake tsayawa takara."

A daidai lokacin da matsalar fashin jiragen ruwan jaura ke daɗa yin tsamari a mashigin tekun Baharmaliya, kamfanonin tsaro masu zaman kansu ke daɗa samun kasuwa da cin ƙazamar riba in ji jaridar Welt am Sonntag. Jaridar ta ce:

"A haƙiƙa dai kamfanonin tsaro masu zaman kansu su ne ke cin ƙazamar riba daga mawuyacin halin da kamfanonin safarar jiragen ruwan jaura ke ciki. Domin kuwa kamfanonin kan karɓi albashin dalar Amirka dubu goma ne a kowane yini daya da dakarunsu ke wa wani jirgi rakiya. Hasali ma dai duka-duka kashi 20 cikin ɗari na yawan basusukan da fashin jiragen ruwan ke haddasawa ne ke kwarara zuwa ita kanta Somaliya, ragowar na kwarara ne a hada-hadar tattalin arziƙi ta yau da kullum."

Mwallafi: Ahmad tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi