Guterres ya yi rantsuwar maye gurbin Ban Ki-moon | Labarai | DW | 12.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guterres ya yi rantsuwar maye gurbin Ban Ki-moon

Antonio Guterres ya zama Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya inda ya ke zama na tara a layi.

Tsohon Firaministan Potugal Antonio Guterres  ya yi rantsuwar kama aiki a ranar Litinin din nan a matsayin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya inda ya ke zama na tara a layi, ya rattaba hannu kan wannan aiki gaban babban taron mai mambobi 193.

Guterres  mai shekaru 67 zai maye gurbin Ban Ki-moon mai shekaru 72 dan asalin Koriya ta Kudu daga ranar daya ga watan Janairu mai zuwa, abin da zai kawo karshen wa'adi biyu na shekara biyar-biyar da  Ban Ki-moon ya yi.

Guterres dai baya ga firaminista tsakanin shekarar 1995 zuwa 2002 ya rike kwamishina na Majalisar Dinmkin Duniyar kan 'yan gudun hijira tun daga shekarar 2005 zuwa 2015.