Gurfanar da jamusawa biyu a gaban kotu a Abuja | Labarai | DW | 03.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gurfanar da jamusawa biyu a gaban kotu a Abuja

A birnin Abujan tarayyar Nigeria, ayau ne aka gurfanar da wasu jamusawa guda biyu da aka zarga da laifuffuka daban daban guda 7 da suka hadar da leken asirin soji da neman bayanai dangane da harkokin tsaron kasar.

An gurfanar da Jamusawan Florian Orpitz mai shekaru 35 da haihuwa,da Andy Lehman mai shekaru 26 da haihuwa ,ne a gaban Alkali Binta Murtala Nyako,tare da wata Ba Amurkiya Judith Asuni mai shekaru 60,wadda ke auren wani Dan Nigeria,da kuma wani dan Nigeria Danjuma Saidu.

An dai zargi jamusawan biyu da shiga Nigeriar ba tare da izini ba,asunan dalibai,ayayinda suka kasashen masu shirya fina finai ne ,ayayinda sauran biyun suka taimaka musu da wuraren zama cikin sirri ,akarkashin wata kungiya mai zaman kanta da Madan Asuni kewa jagoranci.Justice Binta Nyako dai ta dage cigaban Shariar zuwa ranar jumaa,tare da bada umurnin cigaba da tsaresu.