1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gurɓacewra fagen siyasar Niger

June 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuK8

Fagen siyasar Jamhuriya Niger, ya shiga wani saban yanayi ,a sakamakon matakin da Majalisar Dokoki ta ɗauka jiya, na tsige Praminista Hama Amadu daga muƙamin sa,bayan ya share shekaru kussan 8, ya na jan ragamar gwamnati.

Wannan shine karo na 4, da yan majalisar dokokin na ɓangaren adawa ke ajje bukatar sauke shi, daga wannan muƙamin.

Hausawa kance dunia rawar yan mata, na gaba ya koma baya,a wannan karo Ham Amadu ya kasa ƙetare siraɗi ta la´akari da goyan baya, da yan adawa su ka samu daga ɓangaren jam´iyu masu riƙe da ragamar mulki.

Masharahanta a kan harakokin siyasa, na ɗaukar wannan al´amari tamkar wani saban cigaba, a harakokin demokradiya, a nahiyar Afrika.

Yanzu ya ragewa shugaban ƙasa, ya naɗa saban Praminista, kokuma ya rushe Majalisar Dokoki, domin samun saban rin´jaye.

Saidai a cewar Bazum Mohamed, mataimakin shugaban jama´iyar adawa ta PNDS, abun na da kamar wuya shugaba Tanja Mamadu ya aikata hakan.