1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gumurzu a Somaliya

July 6, 2010

Tashin hankali da ke ci gaba da yaɗuwa a Somaliya, ya hallaka mutane da yawa, tsakanin yau da jiya.

https://p.dw.com/p/OBT7
Mayaƙan SomaliyaHoto: AP

A ƙasar Somaliya a ƙalla mutane sha shida suka rasu, yayin da faɗa ta kaure tsakanin mayaƙa masu tsananin kishin Islama su ya su. Rohotonni da suka fito daga Mogadishu a safiyar yau sun bayyana cewa, Faɗan ta yi ƙamarine a lokacin da mayaƙan suka matsa kusa da inda gwamnati ke iko da shi, to amma sai faɗan ta kaure tsakanin su ya su. Wasu mayaƙan daban sun aukawa sojojin gwamnati a arewacin birnin Mogadishu, abinda ya sa aka yi mummunan gumurzu. Kakakin gwamnati Muhamed Abdirrahman ya shaidawa manema labarai cewa bai son iya mayaƙan da aka kashe ba, to amma dai ya son su ma gwamnati an kashe musu soji biyu, da wasu fararen hula uku waɗanda faɗan ta ritsa da su. Mayaƙan dai suna ta auna sansanonin sojojin kiyaye zaman lafiya na tarrayar Afirka dana gurguwar gwamnatin Somaliya. A jiya ne dai ƙasashen yankin suka yi alƙawarin tura ƙarin soji 2000, don samar da tsaro a ƙasar da yaƙi ya ɗai-ɗaita.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu