Guinea za ta bada gudummowar Sojoji zuwa Somaliya | Labarai | DW | 23.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guinea za ta bada gudummowar Sojoji zuwa Somaliya

Ƙungiyar Tarayyar Afirka zata kara yawan dakarunta a Somaliya

default

Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta sanar da kara yawan dakarunta na kiyaye zaman lafiya a Somaliya da gudummowan sojoji daga ƙasar Guinea. Wannan sanarwar tazo ne ayayin, taron ministocin ƙungiyar gabannin buɗe taron shugabanninta na 15 a gobe, taron dake zuwa kasa da makwanni biyu bayan da ƙungiyar al-Shabaab ta Somaliya ta kai hari a Kampala.

shugaban AU  Jean ping ya faɗawa taron manema labaru a birnin Kampala cewar, Guinea ta shirya tura dakarun nata, akan kimanin dubu 8 da yanzu ke girke a Somaliyan dake fama da rigingimu. Ya kara da cewar, suna fatan cikanta dakarun kiyaye zaman lafiyan na haɗin gwiwar zuwa dubu 10.  

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Umaru Aliyu