Guinea ta sassauta dokar hana fita da ta kafa bayan rigingimu a kasar | Labarai | DW | 19.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guinea ta sassauta dokar hana fita da ta kafa bayan rigingimu a kasar

Gwamnatin kasar Gini ta dan sassauta dokar hana fita da ta kafa bayan an samu raguwar zanga-zangar nuna kyamar mulkin shekaru 23 na shugaba Lansana Conte. Wata sanarwa da hafsan hafsoshin soji Janar Kerfala Camara ya bayar ta yi nuna da cewa tun daga yau litinin ´yan kasar ka iya fita daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma. A ranar litinin ta makon jiya aka kafa dokar tabaci a kasar dake yammacin Afirka don dakile jerin zanga-zanga da wani yajin aiki na gama gari da wanda sakamakon sa akalla mutane 100 suka rasu. Shugabannin kungiyoyin kwadago na neman shugaba Conte yayi murabus.´Yan adawa sun ce an kame mutane kimanin 100 tun bayan kafa dokar tabacin.