1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guinea-Bissau ta nada sabon firimiya

Yusuf Bala Nayaya
April 16, 2018

Shugaba Jose Mario Vaz ya bayyana sunan Aristide Gomes a matsayin firaminista a kokari na kawo karshen rikicin siyasa da ya dabaibaye wannan karamar kasa a yankin Afirka ta Yamma.

https://p.dw.com/p/2w9kX
Guinea Bissau Aristides Gomes | 2008
Aristides Gomes ya jima ana damawa da shi a gwamnatiHoto: Getty Images/AFP/G. Gobet

Sabon Firimiya Gomes wanda ya taba rike mukamin na firaminista a tsohuwar kasar da ta zauna karkashin Portugal tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007, a ranar Talata ne za a tabbatar masa da wannan mukami kamar yadda ya bayyana a yayin wata tattaunawa da wakilan kungiyar kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS a Togo.

Ya ce a ranar Alhamis majalisar dokoki za ta koma zama, kana za a yi sabon zaben 'yan majalisar dokoki a watan Nuwamba. Tun dai a watan Agusta na shekarar 2015 ne kasar ta Guinea-Bissau ta shiga rudani na mulki, lokacin da Shugaba Vaz ya sauke firaministansa Domingos Simoes Pereira. Shugaba Vaz dai ya yi ta nada sabbin firaministoci sai dai ba ya nasara saboda gaza samun goyon bayan jam'iyyun siyasa.