1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guillaume Soro ya ƙetara rijiya da baya

Yahouza S.MadobiJune 29, 2007

Wasu mutane da ba a tantance ba, sun kai hari ga jirgin da ke ɗauke da Praministan Cote D´Ivoire.

https://p.dw.com/p/BtvA

A yau juma´a harin ya wakana, minti ɗaya rak, bayan saukar jirgin da ke ɗauke da Guillaume Soro, wanda ya kai ziyara aiki a birnin Bouake, cibiyar tsafin yan tawayen da ya jagoranta, kamin a rattaba hannu a kan yarjejeniyar sulhu ,a birnin Ouagadougou na ƙasar Burkina Faso.

Ya zuwa babu wanda su ka ɗauki alhakin kai wanan hari.

Allan Aliali wani ɗan jaradio da ya hatsarin ya rustsa da shi, a cikin jirgin ya ce Pasenjoji sun gigita, ya kuma tattabar da ganin gawwawaki 4 na mutanen da su ka rasa rayuka, sannan da dama sun ji raunuka.

Saidai shi kansa Guillaume Soro, ya ƙetara rijiya da baya, domin bai samu ba ko ƙwarzane a cikin wannan hari.

Wani wanda ya ganewa idon sa yadda harin ya abku, ya ce rokoki ne, a ka harbo daga nesa , akwai kuma matuƙar wuya a tantance ko su wanene su ka yi wannan aika-aika.

Jim kaɗan bayan kai harin, dakarun yan tawayen FN su ka yi wa filin saukar jiragen samar ƙawanya, su ka kuma tsaurara matakan tsaro a birnin Bouake baki ɗaya.

Daga sassa daban-daban na dunia, an fara yin Allah wadai da wannan hari, wanda ke matsayin maida hannun agogo baya, ga yunkurin samar da zaman lahia a ƙasar Cote D´Ivoire.

Dafa fadar Qai D´Orsay ta ƙasar France, ministan harakokin wajen Bernard Kouchner ya bada ƙarfin gwiwa ga gwamnation Cote D´Ivoire da kuam al´auumar ƙasa baki ɗaya, a hoba sarmar da su ka shiga ta maido da zaman lahia.

Kazalika,tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia, a Cote D´Ivoire ta soki harin da kakkausar lafazi, tare da jaddada goyan bayan ta ga yunƙurin maido da kwanciyar hankali mai ɗorewa a wannan ƙasa da ta yi fama da rikicin tawaye na tsawan shekaru kussan 5.

Tawagar ONUSI ta yi kira ga gwamnati ta ɗauki dukkan matakan da su ka wajabta, domin gano masu alhakin kai wannan hari, domin gurfanar da su gaba ƙulliya.

A wani rahoto da ta buga ranar laraba da ta wuce,hukumar da ke kula da wanzuwar rikita rikia a dunia, wato International Crisis Group, ko kuma ICG a taƙaice,ta yi hannun ka mai sanda a game da ɗigirgiren da yarjejeniyar zaman lahia ke yi, a ƙasar Cote D´Ivoire, ta kuma buƙaci ƙungiyiyon ƙasa da ƙasa, da ƙasashe masu shiga tsakani, su maida himma, wajen tabatar da matakan da a ka cimma, tsakanin gwamnati da yan tawaye ranar 4 ga watan maris , wanda a sakamakon ta, aka naɗa Guillaume Soro Praminista.

Hukumar ta ICG, ta ce an yi yaban ɗanyan mai a game da rikicin ƙasar Cote D´Ivoire, domin har yanzu a na fuskantar tafiyar hawainiya wajen cimma burin da aka sa gaba.