Guido Westerwelle ya shiga kanun mahaura a fagen siyasar Jamus | Siyasa | DW | 13.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Guido Westerwelle ya shiga kanun mahaura a fagen siyasar Jamus

Ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle na fuskantar zargi game da salon aikinsa.

default

Guido Westerewelle na shan zargi daga jamusawa

Saɓanin sauran ministocin harakokin wajen ƙasar Jamus na baya, wanda suka yi ta samun kyakkyawan yabo daga jama´a,Ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a na nuni da cewar ministan harakokin waje mai ci yanzu Gido Westerwelle bai samu karɓuwa ba daga jama´a.

Kamo daga bayyanan da suka jiɓanci siyasar cikin gida, zuwa harakokin diplomatiya da ƙasashen ƙetare ministan harakokin wajen Gido Westerwelle , ya zuwa yanzu bai samu cikkakar karɓuwa ba daga mafi yawan jamsuwa.A halin da ake ciki ya shiga ciki wata mummunar baddaƙƙala a game da wata ziyarara aikin kwanaki shidda da ya kai a  yankin Latine Amurika, inda ake zargin sa da kwasar wata babbar tawaga ta ´yan uwa da aminan arziki, a maimakon ya ɗauki mutanen da suka dace.Masu yiwa Westerwelle wannan zargi, na nuni da cewar bashi bambanta muradin ƙasa da jam´iyarsa ta FDP da kuma alaƙa mutum da mutum tsakanin shi da ´yan uwansa da abokan arziki.

To saidai ministan ya maida martani ya na mai cewar ziyara ce mai mahimmanci ya kawo a Latine Amurika.Ta na da tasiri matuƙa, ga Jamus da diplomasiyarta.Yace ko aka!!! bai damu da soke-soken jam´iyun siyasa ba.

Suma dai kafofin sadarwa sun yi ta bayanai, inda jaridar "Berliner Zeitung" ta rubuta sharhi mai suna "bulaguran Westerwelle tare da iyalinsa".Jaridar tace mafi yawa  daga tawagar ta ministan harakokin waje ta ƙunshi ´yan kasuwa masu tallafawa jam´iyarsa ta FDP kokuma danginsa na jini.

Jam´iyar adawa ta SPD tayi Allah wadai da ɗabi´o´in ministan harakokin wajen na Jamus kamar yadda Andrea Nahles Sakatare Janar na Jam´iyar SPD  ya nunar:

Ƙunbiya ƙunbiya ce kawai domin yin kaso mu raba tsakanin ´yan uwa da aminan arziki.Ya zama wajibi ya fahinci mahimmancin matsayin ministan harakokin waje, wanda aikinsa shine ya ɗaukaka sunan ƙasa a ƙetare a maimakon jam´iyarsa kokuma danginsa.

Shi kuwa Gesine Lötzsch  ɗan majalisardokokin  Bundestag a ƙarsƙashin tutar jam´iyar the Greens mai adawa cewa yayi Westerwelle ya ba Jamus kunya, domin abinda ya aikata cin hanci ne da rashawa:Ya nuna fifiko ga ´yan jam´iyarsa ta FDP, da danginsa.Wannan babakere ne yayiwa ƙasa, saboda haka,za aiya danganta al´amarin da cin hanci da rashawa.

Shidai Guido Westerwelle yayi tsayi tsayin daka domin kare kansa daga wannan zargi. Itama shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel bisa dukan alamu ta bashi goyan baya, tare yin amfani da dokar dake nuni da cewar ,ko wane minista shi ke da ´yancin ƙayyade mutanen da tawagarsa zata ƙunsa a duk lokacin da ya tashi yin bulaguro a ciki ko a wajen Jamus.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Abdullahi Tanko Bala