Guguwar Sidr ta halaka mutane da dama a Bangladesh | Labarai | DW | 16.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guguwar Sidr ta halaka mutane da dama a Bangladesh

Aƙalla mutane 150 sun rigamu gidan gaskiya lokacin da iska mai ƙarfi haɗe da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ake kira Sidr ya ratsa yankin kudu maso yammacin ƙasar Bangladesh. Hukumomi na fargabar cewa yawan waɗanda suka mutu ka iya zarta haka. Yanzu haka dai an kwashe mutane daukacin su kauyawa kimamin dubu 650 zuwa tudun mun tsira. A kasar Indiya ma makwabciyar Bangladesh iskar mai gudun kilomita 240 cikin awa daya ta haddasa mummunar barna. Rahotanni sun ce ƙarfin iskar ya ragu kuma yanzu haka ta doshi arewa maso gabashin Bangladesh.