Guguwar nan ta Krosa ta isa kudu maso gabashin ƙasar China | Labarai | DW | 07.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guguwar nan ta Krosa ta isa kudu maso gabashin ƙasar China

Mahaukaciyar guguwar nan mai hade da ruwan sama da ake yi lakabi da Krosa ta isa yankin kudu maso gabashin kasar China. Yanzu haka dai an kwashe mutane sama da miliyan guda ciki har da daruruwan masu yawon bude ido zuwa tudun mun tsira. A dole hukumomi a yankin sun rufe makarantu da manyan hanyoyin mota da filayen jiragen sama yayin da aka bawa jiragen ruwa kuma umarnin komawa tashoshin su. Kawo yanzu babu labari game da asarar rayuka sakamakon mahaukaciyar guguwar ta Krosa. Akalla mutane 7 suka rasu a Taiwan inda guguwar ta ratsa a jiya.