1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Eleanor ta yi barna aTurai

Abdullahi Tanko Bala
January 3, 2018

Mahaukaciyar guguwar Eleanor ta karade yammacin Turai inda ta katse wutar lantarki da haifar da tsaiko ga tashin daruruwan jiragen sama a nahiyar.

https://p.dw.com/p/2qJAh
Frankreich Winter-Sturm Eleanor
Guguwa da ambaliyar ruwa a FaransaHoto: Getty Images/AFP/F. Lo Presti

Mahaukaciyar guguwa da ke tafiyar kilomita 160 cikin sa'a guda hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya, ta afkawa yammacin Turai a yau laraba, inda ta kada bishiyoyi da kau da jiragen kasa daga layin dogo da kuma kawo tsaiko wajan tashin jiragen sama.

Hukumomi sun bayyana cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da kimanin mutum biyar suka jikkata a kasashen Faransa da Suwizilan.

Bayaga tunkude jiragen kasa daga kan layin dogo, a kasashen Jamus da Suwizilan guguwar ta kuma katse wutar lantarki a yankuna da dama a kasashen Faransa, Birtaniya, Irelan da kuma suwizilan.

A  Jamus an rufe wani bangare na manyan hanyoyin mota dake biranen Duisburg da Jülich da ke yammaci sakamokon bishiyoyi da suka fadi da kuma ambaliyar ruwa sakamakon mahaukaciyar guguwar.