1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gudunmowar musulmin Jamus wa 'yan ci rani

Ƙungiyoyin musulmi na Jamus za su taimaka wajen sajewar 'yan gudun hijira da gaggawa a nan Jamus.

Taron ƙungiyoyin musulmi na Jamus wanda aka kammala a birnin Berlin, ya yi nazari samar da hanyoyin taimaka wa 'yan gudun hijira da ke a ƙasar tare da tallafin gwamnatin Jamus domin sajewa da gaggawa a tsakanin al'ummomin ƙasar.

Fahimtar al'aldu da addinan al'ummar Jamus

Kishi 70 cikin ɗari na yawan 'yan gudun hijira da ke zaune a Jamus waɗanda suka zo daga ƙasashen Yankin Gabas ta Tsakiya galibi musulmi ne. Kuma addadin da ake da shi na ƙungiyoyin musulmi masu yawan a nan Jamus za su iya taimaka wajen samun gaggawar sajewar 'yan ci rani a tsakanin al' ummomin ƙasar a cewar ministan cikin gida na Jamus ɗin Thomas de Maizière, a lokacin da yake yin na a wajen taron.

''Ina fatan dukkanin musulmin da ke zaune a nan ƙasar za su taimaka kana kuma su taka muhimmiyar rawa wajen ganin waɗanda suka zo daga wasu ƙasashen akasari 'yan cirani domin saurin sajewa da al'umma, waɗanda muke kallon cewar za su iya kasancewa jagora a kan al'amarin domin ganin baƙin sun saje da sauran jama'ar.

Shirin ba da tallafin gwamnatin Jamus wa ƙungiyoyin addinai

Deutschland Islamkonferenz 2010 in Berlin Thomas de Maiziere

Gwamnatin dai ta Jamus na tunani tsarin shirin ba da tallafi ga ƙungiyoyn musulmin a gaba dangane da wannan manufofi da aka sama gaba ta hanyar bayar da horo dama tallafi na kuɗaɗ Wannan shi ne irinsa karon farko da aka samu haɗuwar ƙungiyoyin musulmai baki ɗayansu tare da hukumomi domin tattaunawa a kan irin wannan batu na ba da gudunmowa ga yan gudun hijira. Manuela Manuela Schwesig, ita ce ministan kula da harkokin iyalai ta Jamus.

''Musulman da ke zaune a nan Ƙasarmu waɗanda suka riga suka saba da al'adunmu da ɗabi'unmu da kuma addinanmu ba su da wani tababa da mu,kuma za su iya asancewa tafinta na al'adunmu ga sauran baƙin da ke zaman ci trani.Misali a cikin al'adunmu, mace da namiji daidai suke babu nuna bambanci ko wariya.

Ba da horo don samar da aiyyukan yi ga 'yan ci ranin

Dossierbild Dossier Integration Muslime Teil 2

Wani batun da ya kasance da mahimmanci a wajen taron shine na tattara iyalai wuri guda da kuma batun samar da aiyyukan yi ga 'yan ci rani waɗanda ƙungiyoyi da dama da suka halarci taron suka soma yin nazari a kan batun.Ƙungiyoyin musulmin masu aikin hiddimomi na taimaka wa musulmi a Jamus sun kwashe shekaru da dama suna bayar da horro ga matasa na irin aikin raino na yara da tsofi, wanda aƙalla kamar kusan mutum dubu 15 suka ci bmoriyar irin wannan horo wanda kuma da dama daga cikinsu sun samu aiyyukan yi.

Zakariya Altug dan asilin ƙasar Turkiyya ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin musulmi ya yi bayyani kamar haka.

''Idan na dubi batun na ci gaban 'yan gudun hijira ce muna buƙatar samun tallafi a tsakanin al'umma da masalatai da kuma sauran ƙungiyoyi, misali ga abin da a addinance muke kira saddaka wadda musulumin za su ci moriya, ta hanyar samar da kafofi na yin aikatau .