Gudummowar Al′ummar Musulmi a Haiti | Zamantakewa | DW | 30.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gudummowar Al'ummar Musulmi a Haiti

Ƙungiyoyin Musulmi da agajin gaggawa zuwa Haiti

default

Gidan Marayu a Haiti

Duk dacewar ƙasashen musulmi da dama na fama da matsaloli na tattalin arziki da rigingimu dake bukatar agaji, da yawa daga cikinsu sun aike da agaji wa al'ummar Haiti da bala'in girgizar kasa ta ritsa dasu. Haɗaɗɗiyar daular larabawa itace ta fara aikewa da gudummowar dala miliyan 2.6 kwanaki kalilan da aukuwar bala'in, sai kuma Morokko da Turkiyya, sai Saudiyya data bada dala miliyan 50 a gidauniyayar Majalisar Ɗunkin Duniya. Ko yaya sauran musulmi dake fadin Duniya dama nan Jamus ke bada tasu tallafin, kuma menene matsayin gudummowa a musulunci?

Limamamann masallatan Amurka na kira ga al'ummar musulmi dasu taimaka ƙasar Haiti. To sai dai ba wai a Amurka kaɗai ba, musulmi a duk inda suke a faɗin Duniya,kama daga Malasiya zuwa yankin gabas ta tsakiya, suna tattara kudade da kayayyakin agaji a matsayin gudummowarsu wa al'ummar Haiti da bala'in girgizar kasa ta ritsa dasu.

Wata kungiyar agaji ta Red Cresent dake aiki kafaɗa da kafada da kungiyar Red Cross a hadaɗɗiyar daular laraba, ta tara agajin gaggawa na kudi da kayyaki daya kai rabin dala dubu 500, jim kadan da aikuwar girgizar kasar ta Haiti. Reshen ƙungiyar dake Turkiyya a nata bangare ta kaddamar da wani shirin agaji ta fitattcciyar jaridar kasar mai suna Hürriyet...

Haiti Erdbeben Junge

Maraya a Asibiti

A shafinta na yanar gizo kuwa , sama da mako guda kenan babu abunda zaka gani a rubuce sai halin da ake ciki a kasar Haiti da bukatar agazawa al'ummomin wannan kasa. Wannan kungiyar dai na neman agaji ne domin tallafawa marayu dake kasar ta Haiti, kuma ana maraba da tallafi walau daga musulmi ko kuma christoci, kamar yadda Amin Obermüller yayi bayani. Obermüller dai na zama Bajamushe wanda ya karɓi addinin musulunci , kuma ke shugabantar ofishin Hukumar yaƙi da yunwa ta Majalisar Ɗunkin Duniya dake Pakistan. Acewarsa sadaka a musulunci shine mabudin shiga Aljanna...

" ɗaya daga cikin shika shikan musulunci guda biyar shine bayar da zakka, kuma addinin mutum baya cika saida zakka. Kana yana da muhimmanci mutun ya rika bayar da sadaka ko gudummowa ko tallafi"

Türkische Zeitungen in Deutschland Hürriyet

Jardar Hürriyet

A nan tarayyar Jamus dai musulmi da dama sun mayar da martani kan tallafin da ake nemarwa a al'Äummar kasar Haiti, ta hanyoyi daban daban.da ka buɗe shafin yanar gizo na Majalisar musulmi na tarayyar Jamus dai, hoton Haiti ne zaka gani, da yadda zaka iya aikewa da gudummowarka zuwa gidauniya mafi girma da majalisar ta taɓa budewa a kasar. Kazalika kungiyar ta buɗe cibiyoyin bayar da agaji a manyan birane da suka hadar da Berlin da Koln.Tariq Abdel shine shugaban majalisar musulm na birnin koln...

" mun kaddamar da gidauniyyar neman tallafin Euro miliyan biyu. Kuma kawo yanzu mun cimma nasarar tara Euro dubu 60, kuma har yanzu gudummowa na cigaba da zuwa"

Tariq Abdel ya kara dacewar a yanzu haka, kungiyarsu na aiki tare da haɗin gwiwar majalisar Ɗunkin duniya a birnin Port au prince, wajen bada dukkan tallafin daya wajaba.

Mawallafiya: zainab Mohammed

Edita: Abdullahi Tanko Bala