Guantanamo Obama | Siyasa | DW | 14.01.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Guantanamo Obama

Shugaban Amurka mai jiran Gado Barack Obama yayi alkawarin bada umarnin rufe sansanin Guantanamo da zarar ya kama aiki

default

Shugaban Amurka mai jiran Barack ObamaShugaban Amurka mai jiran Gado Barack Obama yace zai bada umarnin gaggawa don rufe sansanin gwale-gwale na Guantanamo da zarar ya hau karagar mulki. Aiwatar da rufe sansanin dai ba abu ne mai sauki ba.


Shi kan sa shugaban na Amurka mai jiran gado Barack Obama ya tabbatar da cewa  rufe sansanin na Guantanamo dake Cuba da kuma kotun soji ta musamman da aka nada domin shariár mutanen da ake tsare da su yana tattare da matsaloli masu sarkakiya."Yace abu ne mai matukar wahalar gaske fiye da yadda jamaá suke tsammani".


Obama yace mai yiwuwa ne a kwanaki 100 na farko na mulkin sa ba zai iya kankare tabon bakin jinin da gwamnatin Bush ta riga ta yi ba, amma yace duk da haka zai iya bakin kokarin sa. "Yace tabbas zamu rufe wannan sansani na Guantanamo".


Babban burin da Obama ya kudirce a zuciyarsa shine cika alkawuran da ya yiwa jamaá a lokacin yakin neman zabe. Sai dai abin tambaya shine yaushe ne zai cika wadannan alkawura ? Jaridar New York Times tace ko shakka babu wannan ba zai samu ba a farko shekara na mulkin Obama, saboda matsalolin suna da yawa.   


A shekarar 2002 aka kafa sansanin na Guantanamo bayan da Amirka ta jagorancin kifar da gwamnatin Taliban a Afghanistan. An kuma kafa sansanin ne da nufin ajiye mutanen da ake zargi da ayyukan taáddanci wadanda gwamnatin Bush tace basu da hurumi a kudirin Geneva na dokar kasa da kasa wadda ta tanadi kula da fursunonin yaki. Bush ya baiyana su da cewa abokan gaba ne amma fursunonin yaki ba.


Bayanai sun nuna cewa mutane 150 daga cikin adadin mutane 248 wadanda ake tsare da su a sansanin na Guantanamo an tabbatar da cewa basu aikata wani laifi na taáddanci ba. Yawancin wadannan mutane da ake tsare su sun fito ne daga kasashen Yemen da China da Libya da Syria da kuma Rasha.


Na farko dai ba zasu iya komawa wadannan kasashe nasu ba, saboda ko dai zaá sake kama su garkame ko kuma a zabtar da su. Ko da yake wasu kasashen turai sun baiyana aniyarsu a hukumace ta karbar wasu daga cikin yan gidan yarin a kasashen su har yanzu ana nan a matakin farko na tattaunawa.


Haza zalika babu tabbas a game da inda zaá rarraba mutanen da ake tsare da su a sansnin na Guantanamo musamman wadanda aka tabbatar da dukkan laifunkan da ake tuhumar su da aikatawa. Misali Sheikh Khaled Mohammed wanda ake tuhuma da kitsa harin 11 ga watan Satumbar shekarar 2001 babu wani gidan yarin sojin Amirka da sauran gidajen yari na kasar da ya nuna aniyar karbar yan gidan yarin na Guantanamo.