Goyon bayan matakan da Papa Roma ya ɗauka a Cocin Katolika | Labarai | DW | 02.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Goyon bayan matakan da Papa Roma ya ɗauka a Cocin Katolika

Limaman Coci-Coci daban-daban sun kare Papa Roma Benedict XVI, game da zargin da akewa shugabanin Cocin katolika da yin lalata da Yara ƙanana a shekaru da dama.

default

Popa Roma Benedict XVI a Fadar Vatican

A saƙonninsu ga mabiya addinin Kirista da sauran al'umman Turai domin bikin Ista, Limaman Cocicoci daban-daban sun kare Papa Roma Benedict XVI, don gane da matsayin daya ɗauka a  game da zargin da akewa shugabanin Cocin katolika da yin lalata da Yara ƙanana a shekarun da dama.

Tunda farko kakakin fadar ta Vertican yace, Papa Roman ya ɗauki wannan bala'i daya aukawa Cocin ta Katolika a matsayin wani gwaji gare shi da kuma Cocin baƙi ɗaya.

Papa Roma wanda yayi bikin na bana kamar yadda aka saba a dandalin Cocin St. Peters, ya kuma gudanar da bikin  tsarkake wasu fada-Fada har 12, dake tunawa da ganawar ƙarshe da Jesu yayi da mabiyan sa su 12, kafin a Gicciye shi a ranar juma'a irin ta yau da Kiristoci ke kira Good Friday. Za'a dai kwashe kwaniki huɗu ana wannan biki da za'a kammala ranar Litinin da bikin Ista. Yanzu haka gwamnatocin ƙasashen duniya daban-daban sun tsaida yau Juma'a da kuma Litinin mai zuwa a matsayin ranakun hutu ga ma'aikata.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Umaru Aliyu