1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Goukkouni Wadai ya yi tayin shiga tsakani a rikicin tawayen ƙasar Tchad

April 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuNS

Tsofan shugaban Tchad Goukouni Wadai,ya yi tayin shiga tsakani, domin cimma masalaha, a rikicin tawayen da ke cigaba da ɓarkewa a gabacin wannan ƙasa.

A ranar jiya talata Goukouni Wadai ya gana da shugaban ƙasar Tchad, Idriss Deby a birnin Libreville, bisa jagorancin shugaban ƙasar Gabon Omar Bango.

Shugabanin 2, sun tanttana halin da ake ciki a ƙasar Tchad ta fannin rikicin tawaye.

Tsofan shugaban ƙasar ya ce a shirye ya ke, ya gana da madugun yan tawayen ƙasar, domin gabatar masu da tayin zaman lahia.

Shugaban ƙasa mai ci yanzu Idriss Deby Itno, yayi lale marhabin da wannan ƙoƙari na Waddai, wanda ke matsayin wata dama, ta cimma zaman lahia mai ɗorewa a ƙasar Tchad.

Goukkouni Wadai na zaman gudun hijira a ƙasashen Lybia da Algeria, tun bayan kiffar da shi daga karagar mulki, a shekara ta 1982.