Goodluck Jonathan ya kori shugaban kamfanin mai na Nijeriya. | NRS-Import | DW | 06.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Goodluck Jonathan ya kori shugaban kamfanin mai na Nijeriya.

Muƙaddashin shugaban Nijeriya ya sallami shugaban babban kamfanin man fetur na ƙasar - NNPC

default

Muƙaddashin shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

Ɗazunnan ne muƙaddashin shugaban Nijeriya Dakta Goodluck Jonathan ya kori shugaban kamfanin Manfetur na ƙasar, wanda aka fi sani da NNPC, Muhammad Sunusi Barkinɗo. Ko da shike kakakin muƙaddashin shugaban ƙasar, wanda ya bayar da sanarwar korar jagorar na NNPC bai yi wani ƙarin bayani game da ɗaukar matakin ba, amma kuma matakin ya zo ne a dai dai lokacin da muƙaddashin shugaban ƙasar ya naɗa mace a matsayin ministar kula da harkokin Man Fetur na ƙasar, inda Deizani Allison Maduekwe, tsohuwar ma'aikaciyar kamfanin mai na Shell zata kula da ma'aikatar man fetur na Nijeriya.

A cewar kakakin muƙaddashin shugaban Nijeriyar, a yanzu Dakta Goodluck Jonathan ne - da kansa, zai kula da ma'aikatar harkokin makamashi na ƙasar, wadda ke da ƙaramin minista. Sauran muƙaman daya naɗa kuwa, sun haɗa da Senata Bala Muhammad a matsayin ministan babban birnin tarayyar Nijeriya, a yayin da Olusegun Aganga kuwa, zai kula da ma'aikatar kuɗin ƙasar. Adetokunbo Kayode ne sabon ministan tsaro a Nijeriyar, a yayin da Farfesa Sheikh Abdallah ya zama ministan kula da harkokin noma.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Umaru Aliyu