Gomnatin Irak ta yi Allah wadai da hotunan Abu Ghraib | Labarai | DW | 16.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gomnatin Irak ta yi Allah wadai da hotunan Abu Ghraib

Gwmanatin kasar Iraki, ta yi tur da Allah wadai, ga hotunan da a ka yada, a kafofdin sadarwa na dunia, inda aka nuna, cin zarafi da wulakanci, da sojojin Amurika ke wa, mutanen da ke tsare a gidan yarin Abu Graib na kasar Iraki.

Gwamantin ta ce zata fara binciken na mussaman, domin tantance gaskiya ga wannan cin zarafi.

Kazalika, ta bayana gamsuwa, da matasyin gwamnatin Amurika, na yin Allah wadai, itama, da wannan aika aika.

A nasu bangaren mutanen kasar Iraki, sun nuna juyayi, tare da tofin allah tsine, ga sojojin Amurika da su ka aikata hakan.