1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Golan da ya fi cin kwallo

Abba BashirJune 12, 2006

Chilavert shine Golan da ya fi cin kwallo a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVO
Jose Luis Chilavert
Jose Luis ChilavertHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Balarabe Mai kano daga Jihar Kanon Tarayyar Najeriya, Malamin ya ce ,daga cikin “Goalkeepers’’ Wato mai tsaron gida ko kuma ace Gola, wane Gola ne ya fi yawan zura kwallo a raga?

Amsa: Golan da ya fi jefa kwallo a raga, shine tsohon golannan dan kasar Paraguay mai suna Jose Luis Chilavert wanda ya ke buga kwallon sa a kulab din Velez Sarsfield na kasar Argentina. Mr Chilavert dai ya zura kwallo a raga har sau 62 kamadai daga wasanni tsakanin manya-manyan kulab na Duniya , zuwa gasanni tsakanin kasashen Duniya.Chilavert dai har ila yau ya na daga cikin yan wasan kwallon kafa na Duniya da suka kware wajen buga Free-kick,kuma har ila yau kwararrene shi wajen buga “Penalties’’ wato bugun daga kai sai gola.Wannan irin yanayi na yawan cin kwallo da Chilavert ya samu kansa , shi ya sa ya zama zakaran gwajin dafi a cikin kwararrun Gololi na Duniya.

An dai haifi Mr. Jose Luis Chilavert a ranar 27 ga wata Juli, 1965. kuma ya bayyana a matsayin dan wasan kwallon kafa tun yana dan shekaru Goma-sha-biyar da haihuwa,a wani Kulab da ake kira da suna Sportivo

Luqueno wanda wannan kulab nasa yana matsayin Division 2 ne wato mataki na 2 kenan Matsayin kwallon kafa. A shekarar 1989 ya yi wasa a kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Paraguay karo na farko, wanda a wannan lokaci tuni ya haye zuwa ga division 1 wato mataki na farko kenan kuma na koli-koli a sha’anin wasan kwallon kafa kuma a wannan lokaci yana wani kulab ne da ake kira da suna San lorenzo. Bayansa ne kuma ya koma kasar Spain inda ya shiga kulab din Argon Club Real Zaragoza, daga nan kuma ya sake dawowa Argentina in da ya shiga kulab dinsa na karshe wato Velez Sarsfield.

Kadan daga cikin nasarori da kuma matsayi da Mr Chilavert ya samu a tarihinsa na wasan kwallo dai sun hada da; Na farko dai an zabeshi a matsayin Gola mafi kwarewa a Duniya a shekarar1995 da 1997 da kuma shekarar 1998. Sannan kuma a shekara 1996 a ka zabeshi a matsayin wanda ya fi kowa kwarewa a wasan kwallo a Gasannin Leaque-leaque na kasar Argentina da kuma yankin South America.

A watan Disambar shekara ta 2003 Chilavert ya sanar wa da Duniya cewar ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa, to amma daga baya sai ya bukaci ya sake dawowa kwallo a kulab dinsa na Velez, in da daga baya ya yi ritaya ta dindindin a ranar 11 ga watan Nuwambar shekara ta 2004, domin kuwa a wannan rana ne ya buga wasan kwallo na karshe kuma na ban kwana wanda kuma a wannan wasa ma ya samu sa’ar zura kwallo a Raga.