1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gogayyar Rasha da Amirka a Gabas ta Tsakiya

December 12, 2017

Shugaba Vladimir Putin da ke ziyara a kasashen Laraba a Masar shi da al-Sissi sun cimma yarjeniyoyin da suka danganci tattalin arzriki da tsaro da diplomasiyya a lokacin da Rasha a yankin ke kara gogayya da Amirka

https://p.dw.com/p/2pEUu
Putin und Al-Sisi in Sotschi 12.08.2014
Hoto: dpa/Alexey Druginyn/RIA Novosti/Kremlin

Yarjejeniyar gina wa Masar tashar wutar lantarki ta farko mai aiki da makamashin nukiliya da za ta samar da karfin megawatt dubu hudu, kan kudi dalar Amirka biliyan 25 da Rashan za ta rantawa Masar, na daya daga cikin batutuwan da shugaban na Rasha yace, mataki ne a aikace na bude sabon shafin alakar cudeni in cudeka tsakanin  kasashen biyu.

  “Na yi amannar cewa, aiwatar da yarjeniyoyin da muka kulla a yau, zai karfafa alakar da ke tsakaninmu fiye da ko yaushe a tarihin alakar Rasha da Masar.”

  Bugu da kari, Rashan ta amince da gina wa Masar ayarin masana'antu a yankin Swiss, wanda hanun jarun da Rashan ta zuba a Masar daga dala biliyan daya da rabi izuwa dala biliyan bakwai.

  Shugaban kasar Masar Abdul Fattah Sisi, wanda Putinn din ya kira da babban abokin kawancensa a yankin, ya yaba wa Rasha kan karar da yace ta jima tanawa kasar Masar.

Syrien russische Kampfjets
Sansanin sojojin Rasha a SiriyaHoto: picture alliance/dpa/Russian Defence Ministry

“Kama daga katafaren madatsan ruwan da kuka gina mana a yankin Aswan da ke kudancin Masar, gami da katafariyar masana'antar karfe da ke Hulwan, ya zuwa yarjejeniyar gina mana tashar makamashin nukiliya, ba abun da za mu yi sai karin godiya da kuma fatar sake karfafuwar wannan alakar da dorewarta.”

   Abu guda da ya rage Putin din bai yi wa Masar ba, shi ne dawo da zirga-zirgar jiragensa a Masar, tun bayan dakatar da su shekaru biyun da suka gabata, biyo bayan tarwatsa jirginta a sararin samaniyar Masar. Inda kan wannan batun shugaban kasar ta Masar ya bayyanan cewa:

 “Muna fata a dawo da zirga zirgar jiragen Rasha a  Sharm el-Sheikh da ma sauran wuraren shakatawa. Saboda fiye da kaso 40% na masu yawon shakatawa a Masar, Rashawa ne.”

 Yarjejeniyar yin amfani da sararin samaniyar Masar da filayen jiragen yakinta da Rashan za ta dinga yi, gami da haduwar ra'ayoyin kasashen biyu, kan rikicin Falalsdinawa da Siriya da Libiya, ya sanya wasu na ganin kamar Masar din na kokarin sauya kawancenta da Amirka da Rashan ne, batun da Ahmad Maragi, wani mai sharhi ke fadi:

“Bana zatan kyakkywar alakar Rasha da Masar za ta rage karsashin tsohuwar alakarta da babbabar kawarta Amirka. Domin Masar, a ko da yaushe, alakarta da kasashe ta ku zo mu tafi tare ne, ba ta a raba gari ba.”