1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobe majalisar dokokin Jamus zata fara muhawwara kan sabon yanayin talauci a cikin kasar

October 18, 2006
https://p.dw.com/p/BufQ
A muhawwarar da ake yi dangane da sabuwar matsalar talauci a Jamus, shugabannin jam´iyar Social democrat sun kare matakan canje-canje a kasuwar kwadago na tsohuwar gwamnatin kawance ta SPD da Greens. To amma a daura da haka babban sakataren jam´iyar CDU Ronald Pofalla ya zargi SPD da laifin karuwar talauci a cikin Jamus. Ita kuwa jam´iyar masu sassaucin ra´ayi ta FDP kira ta yi da a ragewa kananan hukumomin kasar nauyin tafiyar da ayyukan renon yara. Yayin da ´ya´yan jam´iyar neman sauyi suka nema da a daina yin tsimin kudi a ayyukan tallafawa yara da matasa. Ita kuwa majami´ar Katholika ta goyi da bayan wani shirin tallafawa ma´aikata ne.