Gobe Litinin Mbeki zai isa Abidjam | Labarai | DW | 24.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobe Litinin Mbeki zai isa Abidjam

A gobe ne akesaran Shugaban kasar Afrika ta kudu kuma mai shiga tsakani na kungiyar gamayyar Afrika,Thabo Mbeki zai isa kasar Ivory coast,domin wata ziyarar da ake kyxautata zaton zata farfado da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a wannan kasa dake yammacin Afrika.Da ranar gobe nedai ake kyautata zaton Mbeki zai sauka a fadar cinikin kasar watau Abidjam,inda kuma gubar bola ta kashe mutane 7 tare da lahanta dubbai,a yan kwanakin da suka gabata.

Ayayin ziyarar tasa dai zai gana da Shugaba LaurentGbagbo.Kasar ta ivory Coast data kasance akarkashin mulkin faransa a baya dai,ta dare biyu tsakanin arewaci dake hannun yan adawa da kudanci dake karkashin gwamnati,sakamakon yakin basasa daya barke a 2002,a inda yan adawan sukayi yunkurin kifar da gwamnatin Gbagbo.A watan Disamban daya gabata nedai Mbeki,dake sasanta rikicin na Ivory Coast a karkashin inuwar AU ,ya nada Charles Konan Banny a matsayin premier mai rikon gado,kafin a gudanar da zabe.To sai bisa dukkan alamu dai yarjejeniyar da mdd ta cimma a wannan kasa yana neman rushewa,inda manyan jammiyun kasar sukace bazaa gudanar da zaben 31 ga watan oktoba da aka kebe ba.

 • Kwanan wata 24.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5K
 • Kwanan wata 24.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5K