Gobara ta ritsa da 'yan gudun hijira a Jamus
August 10, 2016Mutane 22 da ke zaune a wani gidan 'yan gudun hijirar nan Jamus, sun jikkata sakamakon barkewar gobara da sanyin safiyar wannan Larabar. A cewar mai magana da yawun 'yan sandan da ke jihar Hesse inda nan ne gobarar ta auku, dukkaninsu na samun jinya a asibiti sakamkon hayakin gobarar da suka shaka.
Kawo yanzu dai babu masaniya dangane abun da ya jagoranci gobarar data fara tun cikin daren jiya daga wurin ajiyar kayayyaki dake karkashin ginin, sai dai ana cigaba da gudanar da da bincike.
Rundunar 'yan sanda na Hesse sun shaidar da cewar, jami'an kashe gobara sun cimma gaggauta fitar da mutane 23 dake zaune a gidan 'yan gudun, amma kafin nan 22 daga cikinsu sun jikkata daga hayakin da ya turnukesu.'Yan gudun hijira da ke nan Jamus dai kan fuskanci cin zarafi ta siga daban daban a lokuta da dama.