Gobara ta kashe mutane 36 a Pilipin
June 2, 2017Talla
Harin ya yi mumunar ta'adi ga dandazon jam'a da ke gudun tsira daga kan beni, jami'an tsaro sun janye bayanin farko da ke alakanta harin da ta'addanci, inda ake hasashen maharin da dan fashi. Amma sun tabbatar da mutuwar maharin sa'o'i kalilan bayan bankawa kansa wuta.
A yanzu dai jami'an tsaro sunce fargaba ta fara lafawa, inda ake ci gaba da daukan tsaurara matakan tsaro, a inda harin ya faru dama sauran harabobin da mutane ke taruwa.