Gobara ta hallaka mutane 70 a Mozambik | Labarai | DW | 18.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta hallaka mutane 70 a Mozambik

Gobarar ta tashi lokacin da babbar mota tankar mai ta kama da wuta abin da ya hallaka fiye da mutane 70 cikin yankin tsakiyar kasar Mozambik.

Fiye da mutane 70 sun hallaka sakamakon gobarar da ta tashi lokacin da mota tankar mai ta kama da wuta a yankin tsakiyar kasar Mozambik. Kafofin yada labarai na kasar sun ce akwai kimanin mutane 100 da suka samu raunika, kuma akwai yara a ciki.

Mahukunta sun kaddamar da binciken sanin ko ana sayar da man ne lokacin da lamarin ya faru, ko kuma mazauna yankin ne suka yi wa motar kwantan bauna. Tuni gwamnatin kasar ta Mozambik ta tura ministoci uku zuwa wajen da aka samu gobatar domin gani da ido da sanin hakikanin abin da ya faru.