Gobara ta hallaka mutane 100 a kasar India | Labarai | DW | 10.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta hallaka mutane 100 a kasar India

A kalla mutane kusan dari ne suka kone kurumus a sakamakon wata gobara da ta tashi a wata kasuwar baje kolin kayan lantarki a arewacin India. A cewar baturen yan sanda na birnin Meerut yace a yanzu haka wasu mutanen kimanin 150, suna kwance a asibiti a sakamakon raunukan kuna da suka samu. Rahotanni sun baiyana cewa da yawa daga cikin wadanda suka mutu mata ne da kananan yara, da dama daga cikin su baá iya gane kamanin su.