Gobara ta halaka mutane da dama a Indiya | Labarai | DW | 10.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta halaka mutane da dama a Indiya

Gobarar ta tashi a wajen bauta na mabiya addinin Hindu da ke yankin kudancin Indiya inda mutane kimanin 80 suka halaka wasu fiye da 200 suka samu raunuka.

Kusan mutane 80 sun hallaka yayin da wasu fiye da 200 suka samu raunuka sakamakon gobarar da ta tashi a wajen bauta na mabiya addinin Hindu da ke Jihar Kerala a yankin kudancin kasar Indiya. Wani babban jami'in jihar ya ce lamarin na wannan Lahadi ya faru lokacin da aka samu fashewa. Abin wasa da wuta ya haddasa fashewar lokaci biki na mabiya addnin Hindu.

Akwai yiwuwar samun karin yawan wadanda suka halaka sakamakon gobarar ta Indiya.