Gobara a kurkukun Brazil ya kashe mutane 25 | Labarai | DW | 23.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara a kurkukun Brazil ya kashe mutane 25

Barkewar tarzoma da gobara a wani kurkuku dake kasar Brazil,ya kashe mazauna gidan yarin 25.Rahotanni daga kafofin yada labaru na Brazil na nuni dacewa mazauna gidan kurkun sun balle kofofi domin yin arangama da wasu abokan adawa,a garin Ponte Nova dake jihar Minas Gerais dake kudancin kasar .Kurkun dai na dauke da mutane 170 ne,amaimakon mutane 87 daya kamata su kasance aciki.Msafi yawa daga cikin gawarwakin sun kone kurmus,ta yadda bazaa iya ganesu ba.A yanzu haka dai hukumomin Brazil din sun sanar dacewa komai ya daidaita,ayayinda ake shirin kaurar da wadanda suka cinna wutar zuwa wani kurku mai ingantaccen tsaro.Wannan hadari dai ya auku ne yini uku bayan sanarwar da shugaba Lula Da Silva ya gabatar adangane da shirin yaki da ayyukan tarzoma,inda yace zaa gina karin gidajen kurkuku guda 160,cikin shekaru 4 masu gabatowa.