1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara a Jihar California

Yahouza S.MadobiOctober 23, 2007

Wata mummunar gobara ta ɓarke a jihar California dake ƙasa Amurika

https://p.dw.com/p/BtuH
Hoto: AP

A ƙalla gidaje 600 su ka ƙone ƙurmus, a yayin da dubunan jama´ a su ka tsinci kansu, a halin gudun hijra, a yammacin jihar California dake ƙasar Amurika, a sakamakon ɓarkewar wata mummunar gobara.

Daga arewa da Los Angeles, zuwa iyaka da ƙasar Mexique fiye da jami´an kwana-kwana dubu 2 a ka jera, da kuma jiragen sama masu kishin gobara 30, to amma duk da haka bila´in ya kasance tamkar abunda malam bahaushe ke wa take, gobara daga kogi maganin ki Allah.

Ya zuwa yanzu gobara ta luƙume heka fiye da dubu 40.

A yayin da ya ke jawabi a game da wannan masifa ,Gwamnan jihar California, Arnauld Schwaznegger ya ce jihar sa ta shiga wani mummunan bala´i a game da ya kafa dokar ta ɓace.

Schwazneiger ya kara da cewa.

„Na kafa wannan dokar ta ɓacen domin na yi imanin cewar mu na da halin kawo ƙarshen wannan masifa, tare da sharaɗin gama ƙarfi tsakanin jami´an kashin gobara na jiha da na ƙananan hukumomi ,tare da taimakon gwamnatin taraya“.

Ta la´akari da ci gaba gobara babu ƙaƙƙabtawa, hukumomin jihjar California, sun umurci mutane fiye da dubu 200 na yankin San Diego su ƙauracewa gidajen cikin gaggawa.

Gwamnatin ta yi tanadin filayen ƙwallo da na kasuwanin baje koli, da kuma wasu makarantu, domin samar da matsugunai ga mutanen da su yi asara gidajen su.

A cewar Michel Freman shugaban jami´an kashe gobara na yankin LOs Angeles,duk da matakan da ake ci gaba da ɗaukam, har yanzu al´amarin na ci gaba da ta´azara.

„A cikin daren jiya gobara ta ƙara munana, a yau mu na fuskantar yanayi mai tsanani , wanda ba mu zata ba a baya“.

Cemma dai gobara a jihar California ba saban abu ba ne.

Idan ba a manta ba, a shekara ta 2003, mutane 22 su ka rasa rayuka, sannan gidaje dubu 3, su ka ƙone a sanadiyar gobara.

Wannan gobara da ke ci gaba da hadasa ta´adi a California, ta ɓarke a sakamakon ƙarancin ruwan sama, da kuma kaɗawar iska mai ƙarfi a wannan yanki.

Ƙurraru ta fannin hasashen sararin samaniya sun hango cewa, wannan iska zai ci gaba da kaɗawa har zuwa yammancin yau.