Gobara a filin saukar jiragen samar Amsterdam | Labarai | DW | 27.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara a filin saukar jiragen samar Amsterdam

A daren jiya zuwa sahiyar yau alhamis, wata mumunar gobara da ta kama, a filin saukar jiragen samar Amsterdam a kasar Holand ta yi sanadiyar mutuwar mutane 11.

A yayinda ya kiri taron manema labarai tare da hadin gwiwar jami´an tsaro da yan kwana kwana, magajin garin Schipol ya sanar cewa, dukan mutanen da su ka mutu , mutane ne da ke tsare gidan kurkuku na filin jirgin.

A wannan gidan kurkuku, a na tsare mutanen da aka samu da lefin saffara miyagun kwayoyi ko kuma wanda su ka bukaci shiga kasar Holland, ba tare da cikkakun takardu ba.

Ya zuwa lokacin da gobara ta kama wannan gidan yari na kunshe da yan kasso 350, 43 daga cikin su na sauke inda gobara ta kama.

A wajejen shabiyun daren jiya gobara ta kama ,kuma ya zuwa yanzu, babu masaniyar a game da mussababin kamawar ta.

Jami´an tsaro sun baayana cewa, mai yiwuwa yawan mutanen da su ka mutu ya karu dalili da akwai wasu da ke cikin matsanancin hali, a gidajen assibiti.