Gobara a China ta hallaka mutane da dama
August 13, 2015Talla
Jami'an tsaro a kasar sun killace inda wannan lamari ya wakana a Tianjin da ke arewacin kasar kuma sun mutanen da suka jikkata sun dari hudu.
'Yan sanda sun hana jama'a musamman ma manema labarai kaiwa ga inda abun ya wakana, yayin da wasu al'ummar kasar ke zargin ana share sakonnin da suka sanya kan wannan batu a kafofin sada zumunta irinsu Twitter da Facebook.
Hotuna a shafukan intanet sun nuna yadda gobara ta yi ta'adin gaske a yankin sandiyyar fashewar wasu abubuwa da ake zaton sinadarai ne masu hadari.