1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara a Asibi ta kashe mutane 9 a Rasha

December 10, 2006
https://p.dw.com/p/BuYY

Wajen mutane 9 suka kone har lahira,sakamakon barkewar gobara a wani asibi a garin Siberia,wanda ke zama na biyun irin wannan wuta data ritsa a asibiti a karshen wannan makon kadai a kasar Rasha.Rahotanni daga kasar dai na nuni dacewa,mutane tara ne suka kone har lahira,ayayinda wasu 15 suka jikkata.A kwai kimanin majinyata 223 ,a kwance a wannan asibiti lokacin da gobarar ta kama,kuma har yanzu jamian kashe gobara na cigaba da neman mutane 10,da baasan makomarsu ba da barkewar ´gobarar.