1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka na neman tallafin kuɗi Euro biliyan 45

April 23, 2010

Direktan hukumar bada lamuni ta IMF, ya sanar da cewar nan bada jimawa ba za a fara tattauna tallafawa Girka

https://p.dw.com/p/N4fL
Hoto: picture alliance / dpa

Girka ta bukaci ƙungiyar Tarayyar Turai da hukumar bada lamuni ta IMF da su sake tada batun shirin kuɗaɗen ceto ƙasar da ya kai  Euro biliyan 45. Priminista George Papandreuo ya faɗawa gidan talabijin na Girka cewar, gwamnatinsa na hangen mawuyacin hanya gaba, dangane da haka ne ya zamanto wajibi su samu wannan kuɗin tallafin. Sai dai har yanzu ba a cimma matsaya dangane da ko nawa Girkan zata samu ba.  Direktan IMF Dominique Strauss ya bayyana

cewar yanzu sun fara  fara tattaunawa da hukumomin Girka, dangane da basu tallafi tare da haɗin gwiwar Turai,  kuma nan da 'yan kwanaki masu gabatowa ne za a fara wannan tattaunawar.

A ranar 25 ga watan maris daya gabata nedai aka sanar da yarjejeniyar talafawa Girkar, tsakanin Tarayyar Turai da hukumar bada lamuni ta Majalisar Ɗunkin Duniya watau IMF.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Yahouza Sadissou