Girgizar Tsunamis a Kudancin Asiya | Siyasa | DW | 28.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Girgizar Tsunamis a Kudancin Asiya

Dan-Adam ba ya da ikon dakatar da bala'i daga Indallahi kamar yadda masifar da ta rutsa da yankin kudancin Asiya ta nunar a fili

Barnar da Tsunamis tayi a kasar Indiya

Barnar da Tsunamis tayi a kasar Indiya

Da wuya a iya wayar da kan masuntan dake cikin hali na rudami da rashin sanin tabbas a game da wannan bala’in da ya rutsa dasu a gabar tekun Madras ta kasar Indiya. Domin kuwa girgizar kasar ta faru ne a wani yankin dake da tazarar kilomita 2000 daga Madras, kuma ita kanta igiyar sai da tayi tafiyar awowi biyu kafin ta isa gabar tekun Indiya. Abin tambaya a nan kuwa shi ne me ya sanya aka kasa samun wani da zai gabatar da gargadi a game da tunzurowar igiyar ruwan mai kama da tsaunuka. Saboda duk wanda ya nakalci girgizar kasar da ta faru kamata yayi a ce yana da cikakkiyar masaniya a game da abin da zai biyo baya. A daidai nan ne kuwa take kasa tana dabo inda ake fama da gibi tsakanin matakai na shirin ko-ta-kwana da hasashe na kimiyya. Shi dai bala’i daga Indallahi yana kara nuna wa dan-Adam makurarsa ne a ilimi. Ire-iren wannan bala’i daga Indallahi, Ya-Allah tabo ne daga dutse mai aman wuta ko girgizar kasa ko ambaliyar ruwa, abu ne dake sake mayar da hannun agogo baya ga dukkan ci gaban da dan-Adam ya samu a rayuwarsa a doron kasa. Shi kuma dan-Adam a nasa bangaren ba zai iya tabuka kome ba saboda wannan iko ne na Allah da ya fi karfinsa. Abu daya da Allah Ya yassare masa shi ne daukar matakai na sassauta radadin da kan biyo bayan irin wannan masifa. Wannan manufar ta hada da gabatar da rahotanni da cikakkun bayanai na gaggawa domin yadawa zuwa sassan da lamarin ya shafa. Kuma da hakan ta samu da an samu kafar kubutar da rayukan mutane da dama a kasar Indiya. Ita dai kasar Allah Ya fuwace mata fasaha mai zurfi, inda take da nagartattun na’urorin dake taimaka mata wajen hangen karatowar mahaukaciyar guguwa da sauran masifu daga Indallahi, amma a wannan karon kaddarar ta zo mata a ba zata. A dai yankin tekun indiya da pacific babu wani nagartaccen tsarin da aka tanadar domin gangami a game da karatowar girgizar kasar ta tsunamis mai hadarin gaske ga makomar rayuwar dan-Adam da kewayen halittu, saboda rashin takamaiman hadin kai tsakanin kasashen yankin. Kai hatta a ita kanta kasar ta Indiya ana fama da sabani tsakanin jami’an siyasarta akan wannan batu. Ala-ayyi-halin dai al’umar kasar ba su yi wata-wata ba wajen kai gudummawa ga mutanen da bala’in ya rutsa da su, musamman a lardin Tamil Nadu dake kudancin Indiya, inda suke rarraba wa jama’a a binci da kafa tantuna domin samun mafaka. Irin wannan karimci a kasar da akasarin al’umarta ‚yan rabbana ka wadata mu ne, abu ne dake da muhimmanci, musamman domin sassauta wa jama’a radadin da suke fama da shi.