1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Girgizar kasa ta hallaka mutane 250 a Mexiko

September 20, 2017

Girgizar kasa mai karfin maki 7.1 da ta ratsa kasar Mexiko ta hallaka kusan mutane 250 kamar yadda hukumomi suka nuna.

https://p.dw.com/p/2kKkB
Mexiko Erdbeben Mexiko Stadt
Hoto: picture-alliance/El Universal/B. Fregoso

Kimanin mutane 230 suka hallaka sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 7.1 da ta faru a kasar Mexiko. Lamarin na wannan Talata da ta gabata ya janyo duban mutane sun bazama kan tituna, yayin da wasu mutanen suke taimakon wadanda suka makale a gidaje, bayan faruwar girgizar kasar. Gidaje da dama sun rusa a birnin Mexiko City fadar gwamnatin kasar bayan faruwar wannan girgizar kasa, yayin da aka dauke hasken wutar lantarki. Shi dai wannan birni yana dauke da kimanin mutane milyan 20.

Shugaba Enrique Pena Nieto na kasar ta Mexiko ya ba da umurnin tabbatar da aikon wadanda lamarin ya shafa.

Kasar ta Mexiko mai makwabtaka da Amirka tana cikin wuraren da ake yawaita samun girgizar kasa, inda wadda aka samu ranar 7 ga wannan wata na Satumba ta hallaka kimanin mutane 100.