Girgizar kasa ta auku a kasashen Indonesia da Pakistan | Labarai | DW | 25.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgizar kasa ta auku a kasashen Indonesia da Pakistan

Jim kadan gabanin a fara bukin zagayowar shekara guda da aukuwar ambaliyar igiyar ruwan Tsunami, wasu jerin girgizar kasa sun saka mazauna tsibirin Nias na kasar Indonesia cikin fargaba. Girgizar kasar mai karfin awo 5.4 a ma´aunin Richter ta auku har sau uku a cikin kasa da sa´o´i uku a tsibirin. Ya zuwa yanzu ba bu labari game da irin barnar da girgizar kasar ta haddasa. A arewacin Pakistan ma an fuskanci wata girgizar kasar wadda aka ji motsin ta ma a Islamabad babban birnin kasar. A cikin fargaba mazauna biranen Muzaffarabad da Balakot, inda aka fuskanci mummunar girgizar kasar a cikin watan oktoba, sun tsere daga gidajensu zuwa filin Allah Ta´ala. A kuma halin da ake ciki an gudanar da addu´o´i a Thailand da kasashe makwabta don tunawa da wadanda ambaliyar igiyar ruwan Tsunami ta rutsa da su a bara.