Girgizar kasa mai karfi ta afku a Indunisiya
December 9, 2015Talla
Wata girgizar kasa da ta kai karfin maki bakwai a ma'aunin Richter ta afku a mashigin ruwan Banda Aceh da ke kasar Indonusiya. Ba a dai bayyana yawan mutane da suka rasa rayukansu ko kuma dukiya da ta lalace ba i zuwa yanzu. Sai dai kuma hukumomin Indunusiya sun bayyana cewar babu fargabar afkuwar ingiyar ruwan Tsunami
Ita dai Indunusiya ta saba fuskantar bala'in girgizar kasa mai karfin gaske, inda a shekara ta 2004 mutane dubu 170 suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa hade da igiyar ruwan Tsunami.