1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar- kasa mafi girma a Duniya

Abba BashirDecember 27, 2005

A ina aka yi girgizar- kasa mafi girma a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVf
Girgizar-kasa a Chile
Girgizar-kasa a ChileHoto: dpa

Jama'a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fitone daga hannun malama Abu Yahaya Shuaibu a can birnin Yawunde dake kasar kamaru. Ta ce, don Allah ina so ku sanar da ni ,wai shin a wace kasa ce aka yi girgizar- kasa mafi girma a Duniya?

Amsa : Girgiza-kasa dai mafi girma a Duniya an yi tane a kasar chile, a ranar 22 ga watan mayun shekarar 1960, inda tsawonta yakai awo 9.5 a ma’aunin “Richter” ( wato naurar da ake anfani da ita domin auna girman girgizar-kasa). Bayanai sun tabbatar da cewa sama da mutane 2000 ne suka rasa rayukansu, kuma kimanin mutane 3000 suka samu raunuka, har ilayau kuma kimanin mutane 2,000,000 ne suka yi asarar matsugunansu.

Idan aka koma bangaren dukiyoyi kuwa, wannan kasaitacciyar girgizar-kasa ta yi sanadiyyar asarar dukiyoyi da aka kiyasta kudinsu akan dalar amurka $550,000,000. Har ila yau bala’in bai tsaya nan ba domin kuwa sakamakon wannan girgizar-kasa a kasar chile, ya haifar da ambaliyar ruwa ta tsunami a kasar Hawaii, wadda tayi sanadiyyar mutuwar mutane 61da kuma asarar dukiyoyi da aka kiyasta kudinsu akan dalar amurka $75,000,000. daganan sai ta zarce kasar Japan in da tayi sanadiyyar mutuwar mutane 138,kuma aka yi asarar dukiyoyin da aka kiyasta kudinsu akan dalar amurka $50,000,000. har ila yau bata tsaya anan ba sai da ta fada kasar philippines, inda tai mujazar mutuwar mutane 32 sannan kuma ta ratsa ta yankin west coast na kasar Amurka in da tai ta’adin da aka kiyasta kudinsa akan dalar Amurka $500,000.

Girgizar- kasa mafi muni da take rufawa wannan baya ita ce wacce ta auku a yankin (Prince William Sound) a jihar Alaska ta kasar Amurka, inda wannan girgizar-kasa ta kai awo 9.2 a maaunin “Richter” kuma wannan ya auku ne a ranar 28 ga watan maris shekara ta 1964, wato shekeru hudu kenan bayan waccan da ta auku a kasar chile. Wannan annoba tayi mummunan ta’adi na dukiyoyu kwarai da gaske. Kuma mutane 125 ne suka rasa rayukansu, kuma sakamakon girgizar gasar shima ya haifar da ambaliyar igiyar ruwa ta tsunami da ita ma tayi mummunan ta'adi.