1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

GIRGIZAR KASA A MOROKKO

February 25, 2004
https://p.dw.com/p/Bvli

ZAINAB AM ABUBAKAR:

Kungiyoyin agaji na kasashen duniya na cigaba da kai tallafi wa kasar Morokko sakamakon girgizar kasar safiyar jiya daya ritsa da rayukan mutane sama da 560 ya zuwa yanzu,banda wasu daruruwa da suka jikkata.kungiyar red Cross ta kasar Spain ta tura tawaga daban daban na agaji guda biyar zuwa yankin mediterrian na yankin arewa maso gabashin Moroko inda girgizar kasar ya auku,tare kuma da jamian kashe gobara kimanin 20 daga kudancin kasar ta Spain.Bugu dakari jirgin kasar faransa dauke da jamiaan agaji 15 da kayayyakin agaji na gaggawa sun doshi kasar ta moroko daga kudancin Faransa.Sanarwa daga maaikatar harkokin wajen faransa na nuni dacewa dole ne a taimakawa moroko kann wannan hali data tsinci kanta ciki daga sanyin safiyar jiya.Bugu da kari jirgin kasar Belgium dauke da kayayyakin agaji masu yawa,na shirin daukan hanya zuwa kasar ta morokko.

Hadarin girgizar kasar dai ya auku ne jiya da asubah a garin Al Hoceima,wanda daga wannan lokaci zuwa yanzu an kiyasta cewa kimanin mutane 564 suka rasa rayukansu,ayayinda wasu 300 suka samu raunuka,wanda ya bar hukumomin asibiti da kokawan yadda zasu ceto rayukan wadanda suka jikkata,banda wasu da jamian agaji ke fafutukan ganin cewa an tsirar dasu a raye a karkashin kasa a kauyuka dake wadannan yankin. Wasu kasashen turai ,majalisar dunkin duniya da kungiyar Red Cross tuni suka aike da kayayyaki da jamian agaji zuwa wannan yanki.Kasashen Italia,da Portugal suma baa barsu baya ba wajen aikewa da kayayakin agaji da jamiai zuwa Rabat.Gwamnatin Flanders dake Arewacin Belgium ta sanar da agajin Euro dubu 100,domin samar da runfuna da ruwan sha wa wadanda suka rasa matsugunninsu sakamakon wannan hadari.Ministan harkokin waje na Jamus Joschker Fischer ya bayyana cewa kasarsa a shirye take wajen bada agaji dazai rage wahalan da mazauna yankin ke ciki,a yayinda kungiyar Red Cross dake nan Jamus ta samar da asibitin tafi da gidanka tare da naurara tace ruwan sha.Shi kuwa a nashi bangare sakatare general na Mdd Kofi Annan bayyana damuwansa yayi dangane da wannan asara da akayi.Inda kakakinsa yace Majalisar zata bada kowane agaji da zai rage radadin da mutanen yankin ke ciki sakamakon girgizar kasar. Shi kuwa Paparoma john Poul na biyu addua yayi wa wadanda wannan hadari ya ritsa da rayukansu,kana yayi kira ga kasashen duniya dasu agazawa wadanda suka tsira da rayukansu.A sakon taaziyyarsa Paparoma yayi fatan cewa wadanda suka samu raunuka zasu farfado nan bada jimawa ba,tare da agajin kungiyoyi da kasashen duniya. A halinda ake ciki yanzu dai Daruruwan sojojin Moroko na cigaba da tonon yankin da akayi wannan girgizar kasa,akokarin su na ceto wadanda ya zuwa yanzu baa san makomarsu ba,ayayinda yankin baki daya ke cikin hali mawuyaci sakamakon wannan hadari. Kowane lokaci daga yanzu dai anasaran Salki Mohammed na 6 na Morokko zai isa yankin Imzouren,domin ganewa idanunsa adadin asara da akayi daga wannan girgizar kasa.