Girgizar kasa a lardin Aceh na Indunisiya | Labarai | DW | 07.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgizar kasa a lardin Aceh na Indunisiya

An ba da rahoton cewar akalla mutane guda 25 suka rasa rayukansu kawo yanzu bayan wata girgizar kasar da ta afku a arewacin kasar Indunisiya.

Girgiza kasar mai karfin maki shida da digo hudu da ta kada a lardin na Aceh da ke a arewacin tsibirin Sumatra ta rigito da gidaje da dama,kuma yanzu haka masu aikin ceto na can na  ci gaba da aikin zakulo jama'ar da suka makale a cikin kuraguzan gine-ginen

Lardin dai na Aceh a shekara ta 2014  na daga cikin yankunan da guguwar Tsunami ta hadassa mumanar barna.