Girgizar ƙasa a Indonesia | Labarai | DW | 06.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgizar ƙasa a Indonesia

Rahotanni da suka iso mana daga Indonesia na cewa an sami girgizar ƙasa a yankin tsibirin Sumatra na ƙasar. Girgizar ƙasar mai ƙarfin awo biyar 5.8 ya sanya jamaá sun ɗimauce a yammacin gundumar Sumatra. An ruwaito cewa amon girgizar ƙasar ya dangana da ƙasar Sinhapore dake maƙwabtaka da Indonesia. Girgizar ƙasar ta haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.