Girgizar ƙasa a Ekwado ta kashe mutane | Labarai | DW | 17.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgizar ƙasa a Ekwado ta kashe mutane

Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da aikin ceto domin tantance addadin mutane da girgizar ƙasar ta rutsa da su a yankin kudu maso yamaci na ƙasar.

An ba da rahoton cewar mutane aƙalla guda 41 suka mutu kana wasu da dama suka jikkata a sakamakon wata girgizar ƙasar mai karfin maki 7,1a ma'aunin Richter da ta auku a yankin kudu maso yammaci na Ƙasar Ekwado.shugaban Ƙasar na Ekwado Gorge Glas ya ce sun kafa dokar ta baci.

Wada ya ce ta shafin yankunan da lamarin ya auku domin samun damar ƙaddamar da aiyyuka kai ɗauki ga jama'ar da lamarin ya rutsa da su.